Romans 2

Shariʼar Adalci Na Allah

1Saboda haka, kai da kake ba wa wani laifi, ba ka da wata hujja, gama a duk lokacin da kake ba wa wani laifi, kana hukunta kanka ne, domin kai da kake ba wa wani laifi kai ma kana aikata waɗannan abubuwa. 2Yanzu mun san cewa hukuncin Allah a kan masu aikata waɗannan abubuwa daidai ne. 3Saboda haka saʼad da kai mutum kurum, kana ba su laifi, duk da haka kana aikata abubuwan nan, kana tsammani za ka tsere wa hukuncin Allah ne? 4Ko kuma kana rena wadatar alherinsa, haƙurinsa, da kuma jimrewarsa ne ba tare da sanin cewa alherin Allah yana kai ka ga tuba ba ne?

5Amma saboda taurinkanka da zuciyarka marar tuba, kana tara wa kanka fushi a ranar fushin Allah, saʼad da za a bayyana hukuncinsa mai adalci. 6Allah, “Zai sāka wa kowane mutum gwargwadon aikin da ya yi.”
Zab 62.12; K Mag 24.12
7Ga waɗanda ta wurin naciya suna yin nagarta suna neman ɗaukaka, girma da rashin mutuwa, su za a ba su rai madawwami. 8Amma ga waɗanda suke sonkai waɗanda suke ƙin gaskiya suke kuma bin mugunta, akwai fushi da haushi dominsu. 9Akwai wahala da baƙin ciki ga duk mutumin da yake aikata mugunta: da farko Yahudawa, saʼan nan Alʼummai, 10amma akwai ɗaukaka, girma da salama ga duk mutumin da yake aikata alheri: da farko Yahudawa, saʼan nan Alʼummai. 11Gama Allah ba ya nuna bambanci.

12Duk waɗanda suka yi zunubi a rashi sanin doka, a rashin doka za su hallaka, waɗanda kuma suka yi zunubi ƙarƙashin doka, a ƙarƙashin doka za a hukunta su. 13Gama ba masu jin dokar ne suke da adalci a gaban Allah ba, amma waɗanda suke yin biyayya da dokar, su za a ce da su masu adalci. 14Hakika, saʼad da Alʼummai, waɗanda ba su da dokar, suka aikata abubuwan da dokar take bukata, abubuwan sun zama doka ke nan gare su, ko da yake ba su da dokar. 15To, da yake sun nuna cewa abubuwan da dokar take bukata suna a rubuce a zukatansu, lamirinsu yana kuma ba da shaida, tunaninsu kuwa yanzu yana zarginsu ko kuma yana kāre su. 16Wannan zai faru a ranar da Allah ta wurin Yesu Kiristi zai shariʼanta ɓoyayyun abubuwan da mutane suka yi, yadda bisharata ta furta.

Yahudawa da Doka

17To, kai, da kake kiran kanka Bayahude; in kana dogara ga doka kana kuma taƙama da dangantakarka da Allah; 18in ka san nufinsa ka kuma amince da abin da yake mafifici domin an koyar da kai bisa ga doka; 19in ka tabbata cewa kai jagora ne ga makafi, haske ga waɗanda suke cikin duhu, 20mai koyar da masu wauta, malamin jarirai, domin a cikin dokar ce akwai sani da gaskiya—  21to, kai mai koya wa waɗansu, ba kanka kake koya wa ba? Kai da kake waʼazi kada a yi sata, kana sata? 22Kai da kake cewa wa mutane kada su yi zina, kana yin zina? Kai da kake ƙyamar gumaka, kana sata a haikali? 23Kai da kake taƙama da doka, kana nuna rashin bangirma ga Allah ta wurin karya dokar? 24Kamar yadda yake a rubuce: “Ana saɓon sunan Allah a cikin Alʼummai saboda ku.”
Ish 52.5; Eze 36.22


25Kaciya tana da amfani in kana kiyaye dokar, amma in kana karya dokar, ka zama kamar ba a yi maka kaciya ba. 26In marasa kaciya suna kiyaye dokar, ashe, ba za a ɗauke su kamar an yi musu kaciya ba? 27Wanda ba shi da kaciya ta jiki duk da haka yana biyayya da dokar zai iya hukunta ka, kai da kake karya dokar, ko da yake kana da rubutaccen tsarin dokar an kuma yi maka kaciya.

28Mutum ba Bayahude ba ne in shi Bayahude ne kawai a jiki, haka kuma kaciya ba a waje ko a jiki kawai ba. 29Aʼa, mutum Bayahude ne in shi Bayahude ne a zuci; kuma kaciya ita ce kaciya ta zuci, ta wurin Ruhu, ba ta wurin rubutaccen doka ba. Irin wannan mutum yana samun yabo daga Allah ne, ba ɗan adam ba.

Copyright information for HauSRK